<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><lyrics>[V1]
 1) Yesu Ɗan Allah, yau ka zo!
 Mu fa me za mu yi?
 Mala'iku na sama, ku taimake mu waƙa.
 Yanzu da asubahi, yanzu da asubahi.
 Alhamdu ga Allah har abada!

[V2]
 2) Ya Almasihu, yau ka zo!
 Mu fa me za mu yi?
 Mu durƙusa gabanka, mu yi maka sujada,
 Mu girmama sunanka, mu girmama sunanka.
 Alhamdu ga Allah har abada!

[V3]
 3) Yesu jariri, Mai Ceto,
 Mu ƴaƴanka mun zo,
 Mu ƙanƙananan yara mun kawo maka ranmu
 Mu sa maka albarka, mu sa maka albarka.
 Alhamdu ga Allah har abada!

[V4]
 4) Baitalahmi ne zuciyata,
 Ya Yesu, yau ka zo!
 Ya Ruhu, ina roƙo, ka kawo shi a wurina
 Ya zauna har abada, ya zauna har abada.
 Alhamdu ga Allah har abada!</lyrics>
<title>Yesu Ɗan Allah, Yau Ka Zo LW72</title>
<hymn_number>72</hymn_number>
<author>Handel, George Frederick (1685-1759), Watts, Isaac (1674-1748), Hillsong Worship</author>
</song>